Labarai
ARBA’EEN 1445; Kimanin ‘Yan Uwa 1,000 Suka Halarci Karbala A Bana
A wannan shekarar, an samu ninkuwan adadin maziyartan Imam Husaini (AS) daga bangaren ‘yan uwa almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), a lokacin taron Arba’een din shekarar 1445 (2023), a makwancinsa da ke Karbala.
Ziyarar Arbaeen din, wadda a kowace shekara ‘yan uwa sukan faro ne da yin Tattaki da kafafunsu tun daga birnin Najaf har zuwa Karbala. A wannan shekarar ma, ‘yan uwan sun faro Tattakin ne a safiyar ranar Alhamis 14 ga watan Safar, 1445, bayan shafe yinnai shida suna tafiyar kafa, suka isa haramin Imam Husaini (AS) da ke birnin Karbala da misalin karfe 10 na daren ranar Talata 19 ga Safar.
Wakilin Jagora Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) a yayin Ziyarar ta bana, Shaikh (Dr.) Yusha’u Bin Shaikh, ya bayyana wa CIBIYAR WALLAFA cewa: “Daga Najaf, mun faro Tattakin ne da ‘yan uwan da ba su kai mutum 100 ba, kamar mutum 60 zuwa 70 ne a ranar farko da aka fara Tattakin da safe, amma zuwa yamma adadin ya karu, haka ma washe gari Juma’a adadin ya dada karuwa, haka ma ranar Asabar da Lahadi, kullum adadin na dada karuwa ne.
“Sai ya zama a ranar karshe (Talata) da muka iso Karbala, mun taso (mun nufi Harami) da ‘yan uwa kusan 700 ne, kafin mu shiga Harami kuma mutane suna ta shiga ciki, har aka kai mutane kamar 800 zuwa kusan 900. To kuma bayan mun shiga Harami ‘yan uwa sun sake karuwa sosan gaske a cikinmu, wadanda dukansu ‘yan Nijeriya ne, da suka hada da masu karatu a nan Karbala, da wadanda suke yi a Najaf, da wadanda suka zo daga Iran, da ‘yan sauran wurare, da kuma mu ‘yan Nijeriya da muka zo musamman saboda ziyarar.”
Ya cigaba da cewa: “Ko da yake, har ma da wasu ‘yan kasashen Afirka, musamman ‘yan kasashen Yammacin Afirka, sun zo sun jonu da tawagarmu ta almajiran Sayyid Zakzaky (H), don haka lokacin da muke shiga cikin Haramin, an yi kiyasin an shiga da mutane kusan mutum dubu daya ne. Wanda adadin ya karu a kan na shekarun baya da aka saba zuwa.”
Ba’adin ‘Yan uwa almajiran Shaikh Zakzaky (H) a cikin Haramin Imam Husaini (AS) a lokacin Arba’een din bana
Dr. Yusha’u ya kuma bayyana cewa: “Lokacin da muka zo shiga cikin Ataba, ana ta maganar cewa wai ba a shiga da hotuna ko alami na wani mutum (shaksiyya) ayyananniya, amma mu ko da muka shigo, muka doshi cikin Ataba din, muka je bakin Haramin, sai ga shi su da kansu (masu kula da wajen) suna kiran sunan Jagora, suna gaisuwa da jinjina ga ‘yan uwa a kan irin wannan salo da suka zo da shi a yayin wannan ziyarar tasu ga Abi Abdullah (AS).”
‘Yan uwa suna rike da hoton Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a cikin Haramin Imam Husaini (AS)
Yace: “Dama tun a kan hanya ma, idan muna tafiya, mukan ga idan an jero sunayen manya-manyan Malaman duniya, sai kaga an saka har sunan da Jagoranmu (H). Akan hanyar Najaf zuwa Karbala a wajaje daban-daban mun ga an rubuta sunan Jagora (da hotunansa). Kuma idan suka tashi rubutawa, ba kawai Shaikh suke sakawa masa ba, suna rubuta Ayatullah Shaikh Ibraheem Al-Zakzaky ne.” Yace, “Wannan wani abu ne da ke nuna girmamawa da karramawa ga su Jagora (Allah Ya kara musu lafiya da kariya).”
Nisan da ke tsakanin Najaf zuwa Karbala, tafiya ce ta kimanin Kilomita 78, sai dai kuma su ‘yan uwa sun faro Tattakin ne daga cikin garin Najaf, inda suka shafe wasu Kilomitoci kafin zuwansu inda ake fara kirga Kilomita, sannan kuma bayan isa Karbala, sun cigaba da tafiya da kafa har suka isa Harami, wanda haka yasa za a iya cewa, sun yi tafiya ne na kusan Kilomita 100 da kafarsu don wannan ziyarar.
“Duk da cewa, a wajen Tattaki ba ana kirga Kilomita ba ne, akwai abin da ake kirgawa, ana kirga Amudai ne, ‘Amudi’ kamar wani falwayar wutan lantarki ne, wanda ake sakawa tsakanin nan zuwa nan, su ne ake kira Amudai, kuma su ake kirgawa a matsayin nisan tafiya.” Inji Dr. Yusha’u.
Ya cigaba da cewa: “Amma dai kamar kirgenmu da muka saba na Kilomita, an ce tsakanin Najaf da Karbala kamar 78. To kuma kamar yadda na fada, idan aka hada da inda babu kirgan a Najaf, da kuma inda kirgan ya kare a Karbala, -inda babu Kilomita ko Amudai-, idan aka hada su za a kiyasta za su kai kilomita 10 zuwa 15, kuma idan muka dauka 15 din ne su, za mu ce an taka kusan kilo mita 100 a cikin wadannan yinnai guda shidan kenan.”
Dangane da shigar maziyartan ‘yan uwan cikin Haramin Imam Husaini (AS), Malam Yusha’u ya bayyana cewa: “Lokacin da aka bamu na shiga Harami karfe 10:00 na dare ne, amma sakamakon cinkoso da yawan mutane da aka samu, mun dade a kan layi kafin a kira mu, sai bayan karfe 11:00 na dare muka shiga cikin Haramin don sallama ga Imam Husaini (AS).”
Ya bayyana yadda tawagar ‘yan uwa ta ke tasiri ga tawagogi da sauran mutane da suka fito daga kasashe ta fuskaci daban-daban. Yace: “Idan suka ga tawagar ‘yan Nijeriya ne, tambayar da suke yi shine yaya Jagora yake? Ya Shaikh Zakzaky? Ya lafiyarsa? A wane hali yake ciki a yanzu? Da yawansu da sun gammu tambayarsu kenan akan Jagora da lafiyarsa da halin da yake ciki a yanzu haka. Bayan mun basu amsoshi, sai su yi ta yi masa addu’o’in samun lafiya da damar fita don zuwa neman lafiya a inda ya dace a kasar waje.”
Ya kuma bayyana yadda manyan Malamai daban-daban suke shaukin haduwa da Jagora (H), da yadda suke fatan Allah Ta’ala Ya bashi lafiya ta yadda wata rana zai samu halartan Ziyarar Haramin Imam Husaini (AS) a lokacin Arba’een musamman.
“Ataba Abbasiyya”, wadda ke kula da adadin masu shigowa ziyara a kowace shekara daga kasashen duniya, a bana ta bayyana fiye da mutum Miliyan 22 ne suka halarci taron Arba’een din Imam Husaini (AS) a Karbala.
Ga wasu daga hotunan Tawagar ‘Yan uwan a yayin da Ziyarar ta bana:
Labarai
Yadda Jagora Shaikh Zakzaky Ya Yi Musharaka Da ‘Yan Uwa A Yayin Tattakin Arbaeen Zuwa Karbala
Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya yi musharaka a cikin Tattakin Yaumul Arbaeen da ake yi a ƙasar Iraki, a yau Alhamis 17 ga Safar 1446 (22/8/2024).
Tare da yadda ya rika rabawa al’ummar da ke Tattakin daga Najaf zuwa Karbala hadiyyar abinci da hannunsa masu albarka, don hidimtawa maziyartan Imam Husaini (AS), a Maukibin Ofishinsa da ke Amudi na 1117 a kan hanyar.
Wannan shi ne karo na farko da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya halarci taron Arbaeen din Imam Husaini (AS) a haraminsa da ke Karbala, wanda za a gudanar da taron a ranar Lahadi mai zuwa. Duk da a baya Jagoran ya sha ziyartan makwancin Imam din a lokutan baya, amma ba a daidai lokacin Arbaeen ba.
Za ku iya ganin kuma wasu Hotunan Jagoran, a yayin da ya halarci Maukibin Tariƙatul Husain, a ranar Laraba 16 ga Safar da daddare, inda ya gabatar da jawabi akan yadda sadaukarwar Imam Husaini (AS) ta kawo juyi ga duniyar Musulmi zuwa ga sahihin addini.
Labarai
Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky Ya Isa Birnin Karbala
A ranar Lahadi 12 ga watan Safar 1446 ne Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya bar gida Nijeriya zuwa birnin Karbala Mai Tsarki, don yin Musharaka a taron Yaumul Arbaeen na Imam Husaini (AS) na wannan shekarar, tare da tawagarsa.
Ranar Talata, 14 ga Safar, jami’an Ataba Husainiyya suka tarbe shi a Haramin Imam Husaini (AS) da ke birnin na Karbala. A yayin ziyarar ya gana da Sheikh Abdul Mahdi Karbalai, inda suka tattauna batutuwan da suka shafi yada koyarwar Ahlulbaiti a cikin al’umma.
Wannan ne karo na biyar da Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya je ƙasar ta Iraqi domin ziyarar Limaman Shiriya da Mashhadodinsu ke kasar, sai dai kuma shi ne karo na farko da Jagoran ya je a daidai lokacin da ake gudanar da taron Yaumul Arbaeen, inda miliyoyin maziyarta ke zuwa daga sassa daban-daban na fadin duniya.
Daga tawagar da ke gudanar da Tattaki, musamman daga birnin Najaf zuwa Karbala a duk shekara, akwai tawagar mutanen Nahiyar Afirka, musamman ‘yan Nijeriya, almajiran Shaikh Zakzaky da suke karatu a can, da kuma daruruwan da suke tafiya duk shekara daga nan kasar zuwa kasar Iraq din musamman don wannan, kuma a ranar Lahadin su ma suka fara yin Tattakin daga birnin Najaf, inda suka nufi Karbala, ana sa ran isarsu kafin ko zuwa ranar Arbaeen, wanda za ta fado ranar Lahadi mai zuwa.
Akwai Maukibi da aka tanada musamman don yin hidima ga maziyartan Imam Husaini (AS), wanda ke gudana karkashin ofishin Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a Amudi na 1117, inda dimbin al’umma ke ziyarta suna karban Hadiyya, tare da yi na Jagora addu’a ta musamman.
A gida Nijeriya ma, gobe Laraba ‘yan uwa almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky za su fara gudanar da Tattakin, don misaltawa daga sassa daban-daban na fadin kasar, inda ake sa ran za a rufe a ranar Lahadi, wadda ta dace da ranar Arbaeen din Imam Husaini (AS) na bana, a birnin tarayya, Abuja.
Ga wasu daga hotunan tarbar Jagora, wanda shafin ofishinsa suka wallafa a yau Talata.
Labarai
An Yi Taron Bikin Idil Ghadir A Abuja
Harkar Musulunci a Nijeriya, ƙarkashin Jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), ta gudanar da gaggarumin bikin tunawa da ranar da aka naɗa Imam Ali (AS) a matsayin Khalifa kuma Magajin Annabi (S) a bayansa.
Taron wanda ya gudana a garin Abuja, a ranar Talata 18 ga watan Zulhijja 1445, daidai da 25 ga watan June 2024. Sheikh Zakzaky ne ya zama Babban Baƙo mai jawabi a wajen taron.
Ga Hotunan taron:
-
Makaloli12 months ago
Labarin Fitina Tawayiyya A Takaice
-
Labarai3 months ago
Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky Ya Isa Birnin Karbala
-
Labarai5 months ago
An Yi Taron Bikin Idil Ghadir A Abuja
-
Labarai5 months ago
Jagora Sayyid Zakzaky (H) Ya Yanka Ragonsa Na Layya
-
Bidiyo6 months ago
Shaikh Zakzaky Ya Yi Ta’aziyyar Shahadar Shugaban Iran, Ebraheem Ra’isi
-
Labarai6 months ago
Jagora Sheikh Zakzaky (H) Ya Gana Da Dandalin Ɗalibai A Ranar Tunawa Da Imam Khomeini
-
Labarai6 months ago
A Yayin Bikin Tunawa Da Auren Imam Ali (As) Da Sayyida Zahra (As), Jagora Sheikh Zakzaky (H) Ya Gana Da Dandalin Matasan Sharifai
-
Labarai3 months ago
Yadda Jagora Shaikh Zakzaky Ya Yi Musharaka Da ‘Yan Uwa A Yayin Tattakin Arbaeen Zuwa Karbala