Labarai
Takaitaccen Tarihin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H)
An haifi Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), a unguwar Kwarbai da ke cikin garin Zaria ta jihar Kaduna a ranar 15 ga Sha’aban 1372 Hijiriyya (Miladiyya: 28 April, 1953).
Mahaifinsa shi ne Malam Yaqoub, dan Malam Ali, dan Sharif Tajuddeen, dan Liman Husaini, wanda asalinsu tsatson Manzon Allah Muhammad (S) ne, ta hanyar Imam Hasanul Mujtaba (AS), wanda suka iso kasar Hausa daga garin Shingidi da ke tsohuwar daular Mali ta da.
KARATUN ALKUR’ANI DA LITTATAFAI A ZAURUKAN MALAMAN ZAZZAU
Bayan tasowar Shaikh Zakzaky, ya yi karatun littattafan addini a wajen Malamai daban-daban a garin Zazzau. Ya fara da karatun Alkur’ani a wajen mahaifinsa, da kuma karatun wani littafin Fiqihun Malikiyya mai suna ‘Jiddil Aaziz’ a wajen kakarsa Haajar (da ake kiranta Maikaratu).
Ya kuma cigaba da karatun Alkur’ani (na Allo) a gidan Sarkin Ladanan Zauzzau na lokacin, da kuma wajen Malam Sani Abdulkadir, wanda shi bayan karatun Alkur’ani ya rika hada musu da littafan Fiqihun Malikiyya da kuma Larabci. Banda karatun bai-daya, Shaikh Zakzaky ya rika saka littattafai a gaban Malam Sani Abdulkadir, inda ya sauke littafai irinsu Akhdari, Ishmawi, ‘Dan-Rushdi, ‘Dan-Ashir, Qurdabi, Badamasi, ‘Ya Dalibal Li’irabi, Mulha, Ajruma, Rubu’iyya da sauransu, wadanda duk littafan Fiqihu ne da na Lugga a kasar Hausa a wancan lokacin.
Shaikh Zakzaky (H) ya kuma cigaba da karatu a zauren wani Malami mai suna Malam Isa Na Madaka, inda ya biya littafai masu yawa a gabansa, daga ciki akwai littafin ‘Ta’alimi’, da littafan Iziyyah da Risala, wadanda su littafan Fiqihun Malikiyya ne, da Alburda wanda shi yabon Manzon Allah (S) ne cikin harshen Larabci. Sannan kuma ya kammala karatun Risala, ya yi littafin Askari da Wardi da wasu littafan a gaban Malam Sani Na’ibin Zazzau.
Shaikh Zakzaky, ya kuma yi karatu a wajen Malam Ibrahim Na Kakaki, a wajensa ya kammala littafin ‘Askari’ da ‘Mukhtasar’ da wani littafin Nahwu mai suna ‘Saja’i’, da ‘Alfiyar Dan Maliki’ da ‘Makamatul Hariri’ da wasu littafan Lugan Larabci da Nahwu da dama.
KARATUN NIZAMIYYA A ZARIYA DA KANO
A shekarar 1969, lokacin Shaikh Zakzaky yana dan shekaru 16 da haihuwa, a sannan ya sauke Alkur’ani mai girma, ya kuma sauke mafi yawan littafan Fiqihu da Luga da ake yi a zaurukan Malaman Zazzau a lokacin, sai ya shiga wata makarantar Nizamiyya mai suna “Provincial Arabic School” a Zariya, inda ya yi ta tsawon shekara biyu, ya kammala a 1971.
Bayan ya ci jarabawar wannan makarantar ne ya samu damar zuwa makarantar horar da Malamai ta “School for Arabic Studies” wadda aka fi sani da SAS a Kano, inda ya yi ta daga 1971 zuwa 1975 ya kammala da kyakkyawan sakamako. Da yake ita makarantar SAS ana tarbiyar Malamai ne don su je su koyar a mataki mafi inganci a makarantu a bangaren Larabci da addini, don haka an fi karfafa karatun addini a cikinta.
Sai ya kasance akwai wasu darussan ‘Advance Level’, da mutum yake da zabi ya jona su da karatunsa, sai ya rika zuwa ana musu ‘lesson’ dinsu da yamma (wato ba a ainihin lokacin makarantar ba). Kuma mutum na iya zana jarabawar shiga Jami’a daga wannan ‘Advance level’ din. Sai Shaikh Zakzaky, bisa zabin kansa ya jona da ‘Advance level’ din, inda ya karanta English literature, Economics, Government, Hausa, Arabiyya da kuma Islamic studies. Bayan kammala ta a 1975 kuma ya zana jarabawar ‘Grade II Certificate’, da kuma na ‘Advance Level’ din, duk ya ci su, wannan ya bashi damar shiga Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zariya kai tsaye.
KARATUN LITTATAFAI A ZAURUKAN MALAMAI A KANO
Tsawon shekaru hudun da Shaikh Zakzaky ya yi yana karatun Nizamiyya a Kano, ya kuma rika hadawa da zuwa zaurukan Malamai daban-daban yana cigaba da karatun Littattafan addini da Luggan Larabci.
Ya yi karatu a wajen wani Malami Baqadire mai suna Malam Shawish Abdallah, a unguwar Sagagi, inda a wajensa Shaikh Zakzaky ya sake yin bita da maimaicin da yawa daga littafan da ya biya su tun a gida (Zazzau). Da yake Malam Shawish almajirin Malam Yusuf Makwarari ne, shi kuma Almajirin Sheikh Nasiru Kabara (shugaban dariqar Kadiriyya na Afirka a lokacin), don haka ta wajensa Sheikh Zakzaky ya rika zuwa gidan Sheikh Nasiru Kabara, inda sukan saurari karatun Tafsirin Alkur’ani da kuma littafin Ashafa da yake gabatarwa.
Sannan kuma, akwai Malam Isa (wanda daga baya ya zama Wazirin Kano), yana daga cikin Malaman da suke koyarwa a SAS a lokacin, don haka, Shaikh Zakzaky ya rika karatun littafai a kebe a wajensa, inda ya biya littafai da dama, daga ciki akwai wani littafi mai suna ‘Hukkami’ na Malam Zaqqaqi, wanda yake sharhi ne na ‘Matnil Ghasimiyyah’. Sannan ya karanta ‘Tajridus Sarih’, wanda littafi ne da aka takaice maimaicin Hadisan cikin Sahihul Bukhari, aka yi shi cikin mujalladi biyu.
Har ila yau, a karshen shekarar 1973 bayan Shaikh Zakzaky ya koma zama a unguwar Yola da ke cikin Birnin Kano, ya rika karatu a gaban limamin unguwar Yolan, mai suna Malam Nuhu. Shima a wajensa Sheikh ya maimaita wasu littafan da ya yi a baya ne, irin su ‘Askari’, ‘Muktasar’, ‘Alfiya’ da ‘Makamatul Hariri’.
KARATUN JAMI’A DA FARA DA’AWA
Bayan shigan Shaikh Zakzaky jami’ar Ahmadu Bello (ABU) a shekarar 1976, sai ya tarar da wasu yanayoyi na sako-sako da addini ga dalibai da malamai Musulmin da suke Jami’ar, da kuma yadda ya ga bangaren Kiristoci da masu ra’ayin Kwaminasanci suna hujumi ga addinin Musulunci da kokarin nuna shi a mummunan kama, da ma yadda aka wayi gari baro-baro nizamin da ke mulkin kasar na fada da addinin Musulunci. Ganin wadannan yanayoyin ya sa Shaikh Zakzaky ya fara Da’awar a komawa tsarin Musulunci, wanda ya shafe shekaru uku yana kiran a asirce (a cikin jami’o’in kasar kawai), kafin bayyana da’awar a fili ga al’umma a shekarar 1980.
Tun a watan Disambar 1976 da aka yi wani taron IVC na dalibai Musulmi a garin Gombe, Shaikh Zakzaky ya fara bijiro da bukatar a tattauna dangane da me ya kamata ya zama makomar a kasar nan, ganin cewa ana yayin ra’ayin Kwaminisanci a tsakanin daliban jami’a a lokacin. Ya bijiro da tambaya a tsakanin dalibai Musulmi (MSS), inda a karshe ya bar mutane su je su yi tunani da kansu ba tare da ya fada musu shi abin da yake ganin shi ne mafitan a tashin farko kai tsaye ba. Har zuwa sadda aka hadu a IVC din gaba, sannan fitar musu da hakikar abin da yake nufi.
A IVC na gaba, wanda aka yi a watan Afrilun 1977 a Katsina, nan ne Shaikh Zakzaky ya bayyanawa dalibai Musulmi ra’ayinsa kan cewa, lallai fa ba abin da ya dace ya tafi da rayuwar Musulmi da al’amuran kasar da Musulmi ne mafi rinjayenta kamar tsarin addinin Musulunci. A nan ne ya kirkiri wani bangare da ya saka ma suna ‘External Enlightenment Division’ (EED), inda ya bukaci duk mai sha’awa ya ba da sunansa, saboda za su rika zama bayan kammala kowane taron IVC na MSS, suna karatun addini da kwakkwafe fikirar Musulunci. Daga nan ne masomin Da’awar Harkar Musulunci.
Sai ya zama duk lokacin taron IVC Shaikh Zakzaky kan shirya lakcar musamman don kwakkwafe fikirar Musulmi. Sannan kuma bayan gama taron IVC sukan kara kwanaki tare da mambobin wannan EED din, suna karatun littafan da ke koyar da Fikirar addini da tarbiyar ruhi. Har ya zama an samu wasu daidaiku da suka ji a ransu suna shirye su sallama rayuwarsu a kan kira zuwa ga komawa tafarkin Allah.
A shekarar 1979, wadda ita ce shekarar karshe na karatun Shaikh Zakzaky a jami’ar ABU, suna ma cikin jarabawar karshe, sai wani abu ya faru, wanda ‘yan kungiyar shan giyan kwakwa suka rika amfani da muhalli, da kwanuka, da ababen amfanin Musulmi wajen shan giyarsu, inda su Shaikh Zakzaky suka bi duk matakan da ya dace na kai karansu ga hukumar jami’ar, amma ta ki hana su, don haka, sai su Shaikh suka hana su da karfi, suka farfasa giyan nasu, suka tarwatsa su a wajen.
Wannan abin da ya faru, sai ya jawo hankalin ba kawai hukumar jami’ar ba, har ma fadar Shugaban kasa na lokacin, Olusegun Obasanjo, inda ta turo jami’an tsaro aka girke su a kofar jami’ar, bisa goyon bayanta da ba da kariya ga mashaya giyan. Kuma aka kama Shaikh Zakzaky da gomomin Musulmin kungiyar MSS aka tsare, sai bayan kwanaki aka sake su bisa wani tsararren beli, sannan kuma aka kori wadanda suke rike da mukaman MSS a daidai lokacin daga jami’ar.
Wannan abin ya saka wa Shaikh Zakzaky tunani a kan cewa, ashe duk barnar da ake yi a kasar shi nizamin da ke tafiyar da kasar ne ya ke goyon bayansa, kuma shi ke turo (barnar) cikin al’umma ma. Kuma sai ya zama bayan an sake su, an sake yi musu jarabawar da basu yi ba (sakamakon kama su da aka yin), kuma shi (Shaikh) ya ci jarabawar da kyakkyawan sakamako, amma hukumar makarantar ta ki ta ba shi sakamakonsa sam. Don haka, a lokacin sai Shaikh ya muhimmanta cigaba da da’awarsa na kira zuwa ga komawa addinin Allah (T), da kawar da tsari, ko nizamin da ya sabawa na Allah Ta’ala gabadaya.
SHELANTA DA’AWAR HARKAR MUSULUNCI
A watan Junairu zuwa Febrairun 1980 ne, Shaikh Zakzaky ya samu halartan Jamhuriyar Musulunci ta Iran a karo na farko, a karkashin kungiyar Dalibai Musulmi na kasa (MSS), wanda a lokacin shi ne mataimakin shugaban kungiyar bangaren harkokin kasashen waje. Wannan ziyarar da Shaikh Zakzaky ya kai Iran, ya shafe kusan makonni biyu a can, inda ya dawo a wajajen ranar 14 ga Febrairun 1980 din. Kuma a yayin wannan ziyarar Shaikh Zakzaky ya samu tagomashin ganawada Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, Ayatullah Imam Ruhullah al-Khomeini (QS), inda Imam din ya yi musu jawabi, kuma har Shaikh Zakzaky ya dauko a kaset ya yi tsaraba da shi.
Bayan dawowar Shaikh Zakzaky daga Iran, ya rika shirya lakcoci a manyan jami’o’in kasar nan, da suka hada da Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya (ABU), Jami’ar Jos, jami’ar Lagos, Jami’ar Bayero Kano (BUK), Jami’ar Sokoto da sauransu, inda ya rika ba da labari a kan abubuwan da ya gani a jamhuriyyar Musulunci ta Iran a yayin ziyararsa. Tare da kunna kaset din jawabin Imam Khomaini da ya dauko yana bayani don isar da sakon addini.
A ranar 5 ga watan Afrilun 1980 kuma, Shaikh Ibraheem Zakzaky ya fara shelanta da’awan kira zuwa ga tafarkin Allah a gaban dandazon al’ummar Musulmi a garin Funtua (wadda a yanzu take jihar Katsina). Al’amarin da aka ambace shi da ‘Shelar Funtua’ ko “Funtua Declaration” a Turance.
Duk da cewa Shaikh Ibraheem Zakzaky ba yana matsayin dalibi ba ne a wannan lokacin, amma dai shi ne mataimakin shugaban kungiyar dalibai Musulmi na kasa (MSS), a wannan taron da kungiyar ta gabatar a Funtua, Shaikh Zakzaky sai ya wakilci shugaban kungiyar na lokacin, Ahmad Falaki wanda bai samu halarta ba. Sai Shaikh ya yi amfani da wannan damar, ya karanta wani jawabi da a ciki yake bayyana tawaye ga duk wani tsari da ya sabawa na Allah (T), ya kuma bayyana goyon bayansa ga Allah (T) da shari’arsa, ya kuma yi kira ga al’ummar Musulmi da su yi tawaye ga tsarin mulkin kasar wanda ya yi hannun riga da tsarin Allah (T), tare da kiran mutane kan su zo a hadu a yi yunkurin tabbatar da addini da shari’ar Allah (T) na Alkur’ani a kasar nan.
HARE-HAREN MAHUKUNTAN NIJERIYA GA SHAIKH ZAKZAKY
Wannan shelar da Shaikh Zakzaky ya yi, ta karbu a cikin al’ummar Musulmin Nijeriya, wannan yasa nan da nan hukumar kasar ta fara kokarin kawar da shi da da’awar tasa, ta hanyar kamu, da afkawa, da kuma kisa ma a wasu lokutan, kamar haka;
1- Gwamnatin Alhaji Shehu Shagari, ta kama Shaikh Zakzaky (H) da ‘yan uwa uku a ranar 15 ga Afrilun 1981, lokacin da suka je taron IVC na dalibai Musulmi a Sokoto, inda bayan tsare su da aka yi a Kurkukun Sakkwato na tsawon watanni 5, a watan Satumbar 1981 aka kawo musu waranti cewa kotu ta daure Shaikh Zakzaky shekaru 4 bisa laifin yin wa’azi ba tare da lasisi ba, sauran mutum ukun kuma shekaru biyu-biyu. Sai a ranar 15 ga Afrilun 1984, bayan shafe shekaru uku cur a tsare a kurkukun Inugu sannan Allah ya kaddara fitowar Shaikh Zakzaky.
2- A farko-farkon watan Disambar 1984 din, Janaral Muhammadu Buhari ya hambare gwamnatin Shehu Shagari, a wannan watan kuma ya kama Shaikh Zakzaky ya tsare shi a Interrogation Center da ke Lagos na tsawon watanni uku, tun daga Disambar nan har zuwa watan Maris 1985, bayan haka, sai suka mai da Shaikh din kurkukun Kiri-kiri inda ya shafe watanni biyar a can yana tsare. Har ya zama an haifa wa Shaikh Zakzaky yaronsa na farko mai suna Muhammad, lokacin yana tsare a wannan kamun ne. Sai a farkon watan Satumbar 1985 bayan Babangida ya hambare gwamnatin Buhari sannan ya saki Shaikh Zakzaky.
3- A Ranar Asabar 28 ga watan Maris 1987, sai shi ma Janaral Ibrahim Badamasi Babangida ya kama Shaikh Ibraheem Zakzaky, tare da matarsa da wasu ‘yan uwa maza da mata, a lokacin matar tana da cikin ‘yarsa ta biyu mai suna Nusaibah, don haka ba ta jima ba suka sake ta. Shi kuwa Shaikh Zakzaky sun tsare shi a kurkukun Kaduna na tsawon watanni takwas, sannan suka mayar da shi kurkukun Fatakwal suka tsare shi har zuwa ranar 28 ga watan Nuwambar 1989 Allah Ya nufi fitowarsa, bayan shafe shekaru kusan uku a tsare.
4- A karo na biyu a mulkin Janaral Badamasi Babangida, a watan Nuwambar 1991 jami’an tsaron farin kaya suka kama Shaikh Ibraheem Zakzaky a filin jirgin saman Aminu Kano, daidai lokacin zai je taro a London. Inda suka tsare shi a ofishinsu da ke Kano na kwana daya, kashegari suka tafi da shi hedikwatansu da ke Lagos, suka tsare shi kusan kwanaki hudu da sunan bincike, daga karshe Allah ya kubutar da shi a wannan lokacin aka sake shi.
5- A ranar Alhamis 12 ga watan Satumbar 1996, Janaral Sani Abacha ya turo jami’an tsaro har gida suka kama Sheikh Ibraheem Zakzaky suka tafi da shi Kaduna, suka tsare a hedikwatan ‘yan sanda. Kashegari Juma’a da ‘yan uwa suka fito Muzaharar kira a saki Malaminsu, sai jam’an tsaro suka bude wuta a daidai kofar Doka a garin Zariya, nan take suka kashe mutum 15, suka ji wa gomomi rauni. Bayan kwanaki biyu da kama su Shaikh, ranar Asabar, suka kai shi kurkukun Fatakwal (Port Harcourt) babban birnin jihar River, suka tsare shi tsawon watanni tara a can, sai a ranar 2/6/1997, suka dawo da shi kurkukun Kaduna suka cigaba da tsare shi har zuwa ranar 18 ga Disamba 1998, bayan shafe shekaru biyu da kusan rabi yana tsare sannan suka sake shi. A lokacin an kama Shaikh tare da wasu ‘yan uwa, bayan kamun kuma an cigaba da kama ‘yan uwa a fadin kasar, tare da cigaba da budewa almajiransa wuta a lokutan Muzaharori da tarurruka a tsawon mulkin Abacha da lokacin rikon kwaryan Abdussalami Abubakar.
6- A ranar 14 ga Disambar 2015 sojojin Nijeriya bisa umurnin shugaban kasa Muhammadu Buhari suka sake kama Shaikh Ibraheem Zakzaky, bayan sun kwana biyu suna bude wuta a kan almajiransa a gidansa da ke Gyallesu da kuma Husainiyyah Bakiyatullah da Darur Rahma, inda suka kashe kusan mutum dubu. Bayan sun kashe ‘ya’yansa a gabansa, sun harbi matarsa da shi kansa, suka kama shi suka tafi da shi cikin jini, suka tsare a wajen jami’an tsaron farin kaya (DSS) a Abuja da Kaduna, daga karshe suka mai da shi da matarsa kurkukun Kaduna. Sai a ranar 28 ga watan July, 2021, bayan shafe kimanin shekaru shida da rabi ana tsare da su, sannan kotu ta wanke su daga dukkan tuhumomin da gwamnati ke musu, ta sake su ba tare da wani sharadi ba.
7- A tsawon wadannan shekaru kusan 45 na Da’awar Harkar Musulunci, gwamnatin Nijeriya ta rika kai hare-hare daban-daban a lokuta daban-daban a kan almajiran Shaikh Zakzaky (H), tun tana amfani da ‘yan tauri da masarautun gargajiya, ta koma amfani da ‘yan Izala (Wahabiya), ta koma fitowa kai tsaye ta bude wuta ta hanyar jami’an tsaronta. A yayin da ta sha yunkurin kashe Shaikh Zakzaky a lokuta daban-daban, daga ciki akwai lokacin fitina Tawayiyya inda suka yi manyan yunkuri har karo biyu; karo na farko a cikin masallacin BUK, karo na biyu a makarantar Technical, da kuma lokacin Shugaban kasa Alhaji Umar Musa ‘Yar’adua, da suka yi nufin jefa bom a gidan Shaikh Zakzaky, shi ma Allah Ta’ala ya kare. Da kuma lokacin Goodluck Ebele Jonathan da suka yi gomomin yunkurin kai wa Shaikh Zakzaky hari a gidansa da daddare ko a kan hanyar zuwansa Husainiyyah a ranakun zuwa bayar da karatu.
MALAMAN SHAIKH ZAKZAKY NA IMAMIYYAH
Tun zuwan Shaikh Zakzaky jamhuriyar Musulunci ta Iran a shekarar 1980, ya dawo da tsarabar wasu daga littafan Imamiyya, irin su “al-Istibsar” da “Attahzib” na Shaikh Dusi, da “al-Mabsud”, da littafan su Shaikhud Da’ifa, da na Muhaqqiqul Hilli (RH) da sauransu, tunda yana da shimfidar karatun gida, ya rika bitansu a kan kansa a lokutan da yake tsare a kurkukun da aka rika kama shi a wannan tsakanin. In an lura, tsakanin shekara goman 1980 zuwa 1990 Shaikh Zakzaky ya shafe shekaru kusan bakwai ne a tsare a kurkuku daban-daban.
Har zuwa shekarar 1990, da ya fara zuwa karatu a Hauza Ilmiyyah da ke Ghana, inda ya rika karatu a wajen wani Malami mai suna Sayyid Tabataba’I, wanda a lokacin ya zo Afirka da nufin Tablig (isar da sakon addini), musamman sun bi littafin Biharul Anwar da wasu littafan suna bahasinsu. Tsawon kimanin shekaru uku, duk karshen wata Shaikh Zakzaky kan je ya yi kwanaki ya dawo.
Bayan haka kuma, ba jimawa da fitowarsa daga Kurkukun kamun Abacha, sai ya fara zuwa Daura Ilmiyyah a jamhuriyar Musulunci ta Iran, yana karatu a wajen Malamai daban-daban. Daga cikinsu akwai Shaikh Jaafarul Hadi, wanda ya karantar da Shaikh Zakzaky fannoni daban-daban, musamman Aqida, da kuma Usul.
Ya kuma yi bahasi dangane da littafin Nahjul Balgaha na Amirulmuminin (AS) gabadayansa a wajen wani Malami mai suna Shaikh Suwaidi. Wannan ya faru ne tun kafin Shaikh din ya fara karantar da littafin Nahjul Balagha. Da kuma Farfesa Dahiri, wanda Sheikh Zakzaky ya yi karatun Mandiq a wajensa. Sannan ya karanci Tafsirin Alkur’ani, inda suka bi Tafsirin Ayatullah Jawadi Amuliy (Tasneem fi Tafsirul Qur’an) da wani Malami wanda shi yana daga cikin jigon aikin tarjamawa da rubuta Tafsirin a lokacin, mai suna Shaikh Haaqani.
Tun ana kan tarjama shi zuwa Larabci, kafin a kai ga bugawa suka yi bitansa. Kila wannan ya taimaka wajen sanyawa Shaikh Zakzaky tasiri, inda a wani lokaci a farkon gabatar da Tafsirinsa zagaye na uku, ya bayyana cewa, hatta Tafsirin Alkur’ani yana bukatar Taqalidi, saboda haka, shi ya dauki Ayatullah Jawadi Amuli a matsayin Marj’insa a bangaren Tafsirin Alkur’ani.
Har ila yau, cikin Malaman da suka karantar da Shaikh Zakzaky, akwai Sheikh Tabasi da ke Qum, da kuma Ayatullah Ahmadi, da Sheikh Munzir Hakeem, da Sayyid Ridawiy da sauransu.
Duk lokacin da Sheikh Zakzaky ya je wannan Dauran Karatun a Iran, yakan shafe kimanin kwanaki 40 ne a can yana karatun kafin ya dawo, yakan je kusan duk shekara ko bayan watanni, tun wajajen shekarar 2000 har zuwa shekarar 2015 kafin Waki’ar Buhari ta Zariya.
KARANTARWARSA
Shaikh Ibraheem Zakzaky ya rika karantar da Tafsirin Alkur’ani da kuma wasu littafai, tun a shekarunsa na Jami’a, musamman kuma daga shekarar 1980 bayan shelanta da’awa, ya fara karantar da almajiransa Tafsirin Alkur’ani, inda suke karantarsa tare da aikata shi kai tsaye. Wadanda suka shaidi farkon Harkar nan, sun bayyana cewa, a wancan lokacin, idan aka karanta Aya daya, da Allah Ta’ala ke umurni da a yi sallar dare, sai a tsaya a ga an tsayu da sallar daren kafin a cigaba da dauko wasu Ayoyin ana bitansu. Idan aka karanta Ayar da Allah Ta’ala Ya yi umurni ga Annabi (S) akan ya gargadi mutane, sai a tashi a je cikin gari a rika tunatar da mutane a kan manufar Allah Ta’ala na yin Dan Adam a doron kasa, da bukatuwa zuwa ga komawa tsarin Allah da shari’a da Alkur’ani.
Da yake an rika kama Shaikh Zakzaky ya shafe shekaru a Kurkuku, hatta a Kurkukun, Shaikh Zakzaky ya rika karantar da mutane daban-daban littafan addini idan suka nuna sha’awa, ko kuma idan ya zama kamun ya hada da ‘yan uwa, kamar kamun Waki’ar Kafancan (na lokacin Babangida), wanda Shaikh din ya rika koyar da ‘yan uwa karatun Alkur’ani da Tafsirinsa. Haka ma a lokacin kamun Abacha, bayan dawo da su kurkukun Kaduna, ya rika karantar da almajiransa da suke tare da shi littafan addini, irin su littafin Tahrirul Wasila na Imam Khomaini, da littafan Alkhlaq da na Aqida da sauransu.
Bayan mallakar Fudiyyah Islamic Center a Zariya a shekarar 2002, Shaikh Zakzaky ya fara gabatar da Tafsirin Alkur’ani, inda kowa da kowa ke iya halarta a duk ranar Laraba a tsawon shekara, a yayin da idan Ramadan ya zo, sai a koma yi kullum, har ya zama an sauke Tafsirul Mubin a karon farko tare da sirkawa da ruwayoyi daga littafan Ahlis Sunnah, saboda kokarin fahimtar da mutanen da ake tare da su.
Bayan haka, Shaikh ya sake dauko Tafsirin a karo na biyu, tare da takaita bayanai, har zuwa sadda aka shiga Suratul Ahzab, sannan ya fara fadada bayanai da karanto ruwayoyi daga A’immatu Ahlulbaiti (AS) dangane da ma’anar Ayoyi. Bayan an yi sauka na biyu, a yayin da aka faro sauka karo na uku kuwa, sai ya zama gabadaya Tafsirin ana yinsa ne daga littafan Tafsiran Imamiyya, tare da fassara kowace Aya da ruwayoyin da aka samu daga A’imma (AS) dangane da fassararsu. Sai dai ana cikin Suratul Aali Imran ne, aka yi waki’ar Buhari a 2015, wanda zuwa yanzu ba a cigaba ba.
Har ila yau, Shaikh Zakzaky ya rika karantar da littafin Nahjul Balagha a duk ranar Litini a Fudiyyah Islamic Center, har zuwa shekarar 2010 bayan an samu Husainiyyah Bakiyyatullah, karatun ya dawo nan.
Baya ga wannan, Shaikh Zakzaky na karantar da wasu daga almajiransa karatuttuka kebantacce (Khaas), inda sukan shafe wata guda suna gabatarwa, kusan kowace shekara sau biyu. Daga darussan da yake basu akwai bangaren Fiqihu, da Aqida da Akhlaq. A yayin da kuma duk ranar Talata yake zama tare da ‘yan uwa mata, suma yana karantar da su ilmummukan addini daban-daban, zaman da aka fi sani da ‘Majlis’.
KAMMALAWA
A yanzu haka, Shaikh Ibraheem Zakzaky yana da shekaru 73 a Hijiriyya, a Miladiyya kuma kimanin shekaru 70 kenan. Matarsa daya ce, Malama Zeenah Ibrahim, sun haifi ‘ya’ya tara (9) da ita; maza 7, mata 2. Mutum shida daga cikin ‘ya’yan nashi, Allah Ta’ala Ya azurta su da samun Shahada; uku daga cikinsu; Ahmad, Hamid da Mahmud, sun yi shahada a lokacin Waki’ar Muzaharar Quds ta 2014, sai kuma Hammad, Ali da Humaid, wadanda sojoji suka kashe su a gaban mahaifansu a lokacin da suka kawo hari a gidan Shaikh din a shekarar 2015.
Yanzu akwai Nusaiba da Suhaila a raye, sai kuma babban yaron Shaikh Zakzaky, mai suna Muhammad, wanda yake da mata daya da yara biyu; Husain (Naadir) da kuma kanwarsa Naseemah (Fatimah).
Wallafawa: Cibiyar Wallafa Da Yada Ayyukan Shaikh Zakzaky (H).
Tuntuba: cibiyarwallafa@gmail.com
Website: www.cibiyarwallafa.org
Facebook: www.facebook.com/cibiyarwallafa2016
Labarai
Yadda Jagora Shaikh Zakzaky Ya Yi Musharaka Da ‘Yan Uwa A Yayin Tattakin Arbaeen Zuwa Karbala
Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya yi musharaka a cikin Tattakin Yaumul Arbaeen da ake yi a ƙasar Iraki, a yau Alhamis 17 ga Safar 1446 (22/8/2024).
Tare da yadda ya rika rabawa al’ummar da ke Tattakin daga Najaf zuwa Karbala hadiyyar abinci da hannunsa masu albarka, don hidimtawa maziyartan Imam Husaini (AS), a Maukibin Ofishinsa da ke Amudi na 1117 a kan hanyar.
Wannan shi ne karo na farko da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya halarci taron Arbaeen din Imam Husaini (AS) a haraminsa da ke Karbala, wanda za a gudanar da taron a ranar Lahadi mai zuwa. Duk da a baya Jagoran ya sha ziyartan makwancin Imam din a lokutan baya, amma ba a daidai lokacin Arbaeen ba.
Za ku iya ganin kuma wasu Hotunan Jagoran, a yayin da ya halarci Maukibin Tariƙatul Husain, a ranar Laraba 16 ga Safar da daddare, inda ya gabatar da jawabi akan yadda sadaukarwar Imam Husaini (AS) ta kawo juyi ga duniyar Musulmi zuwa ga sahihin addini.
Labarai
Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky Ya Isa Birnin Karbala
A ranar Lahadi 12 ga watan Safar 1446 ne Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya bar gida Nijeriya zuwa birnin Karbala Mai Tsarki, don yin Musharaka a taron Yaumul Arbaeen na Imam Husaini (AS) na wannan shekarar, tare da tawagarsa.
Ranar Talata, 14 ga Safar, jami’an Ataba Husainiyya suka tarbe shi a Haramin Imam Husaini (AS) da ke birnin na Karbala. A yayin ziyarar ya gana da Sheikh Abdul Mahdi Karbalai, inda suka tattauna batutuwan da suka shafi yada koyarwar Ahlulbaiti a cikin al’umma.
Wannan ne karo na biyar da Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya je ƙasar ta Iraqi domin ziyarar Limaman Shiriya da Mashhadodinsu ke kasar, sai dai kuma shi ne karo na farko da Jagoran ya je a daidai lokacin da ake gudanar da taron Yaumul Arbaeen, inda miliyoyin maziyarta ke zuwa daga sassa daban-daban na fadin duniya.
Daga tawagar da ke gudanar da Tattaki, musamman daga birnin Najaf zuwa Karbala a duk shekara, akwai tawagar mutanen Nahiyar Afirka, musamman ‘yan Nijeriya, almajiran Shaikh Zakzaky da suke karatu a can, da kuma daruruwan da suke tafiya duk shekara daga nan kasar zuwa kasar Iraq din musamman don wannan, kuma a ranar Lahadin su ma suka fara yin Tattakin daga birnin Najaf, inda suka nufi Karbala, ana sa ran isarsu kafin ko zuwa ranar Arbaeen, wanda za ta fado ranar Lahadi mai zuwa.
Akwai Maukibi da aka tanada musamman don yin hidima ga maziyartan Imam Husaini (AS), wanda ke gudana karkashin ofishin Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a Amudi na 1117, inda dimbin al’umma ke ziyarta suna karban Hadiyya, tare da yi na Jagora addu’a ta musamman.
A gida Nijeriya ma, gobe Laraba ‘yan uwa almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky za su fara gudanar da Tattakin, don misaltawa daga sassa daban-daban na fadin kasar, inda ake sa ran za a rufe a ranar Lahadi, wadda ta dace da ranar Arbaeen din Imam Husaini (AS) na bana, a birnin tarayya, Abuja.
Ga wasu daga hotunan tarbar Jagora, wanda shafin ofishinsa suka wallafa a yau Talata.
Labarai
An Yi Taron Bikin Idil Ghadir A Abuja
Harkar Musulunci a Nijeriya, ƙarkashin Jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), ta gudanar da gaggarumin bikin tunawa da ranar da aka naɗa Imam Ali (AS) a matsayin Khalifa kuma Magajin Annabi (S) a bayansa.
Taron wanda ya gudana a garin Abuja, a ranar Talata 18 ga watan Zulhijja 1445, daidai da 25 ga watan June 2024. Sheikh Zakzaky ne ya zama Babban Baƙo mai jawabi a wajen taron.
Ga Hotunan taron:
-
Makaloli12 months ago
Labarin Fitina Tawayiyya A Takaice
-
Labarai3 months ago
Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky Ya Isa Birnin Karbala
-
Labarai5 months ago
An Yi Taron Bikin Idil Ghadir A Abuja
-
Labarai5 months ago
Jagora Sayyid Zakzaky (H) Ya Yanka Ragonsa Na Layya
-
Bidiyo6 months ago
Shaikh Zakzaky Ya Yi Ta’aziyyar Shahadar Shugaban Iran, Ebraheem Ra’isi
-
Labarai6 months ago
Jagora Sheikh Zakzaky (H) Ya Gana Da Dandalin Ɗalibai A Ranar Tunawa Da Imam Khomeini
-
Labarai6 months ago
A Yayin Bikin Tunawa Da Auren Imam Ali (As) Da Sayyida Zahra (As), Jagora Sheikh Zakzaky (H) Ya Gana Da Dandalin Matasan Sharifai
-
Labarai3 months ago
Yadda Jagora Shaikh Zakzaky Ya Yi Musharaka Da ‘Yan Uwa A Yayin Tattakin Arbaeen Zuwa Karbala