Connect with us

Labarai

Jawabin Jagora Shaikh Zakzaky Kan Muzaharar Quds 1444/2023

Published

on

Bismillahir Rahamanir Raheem.
Wasallallahu Ala Sayyidina Wa Nabiyina wa Habibi Qulubina Abul Qasimi Mustapha Muhammad wa ala alihid Dayyibinad Dahirinal Ma’asumiyn.

Assalamu Alaikum wa Rahmatullahi Ta’ala wa barakatuh.

Yau Laraba 21 ga watan Ramadan, hijira 1444. To, zan dauki wadannan mintoci ne na tunatar da mu cewa, yau fa ranar Shahadar Amirulmuminin (AS) ne. Wanda aka sara ranar 19 ga watan Ramadan, ruhinsa tsarkakka ya bar gangan jikinsa a yammacin 21 ga watan Ramadan. Saboda haka muna taya al’umma jaje. Muna cewa, “Aazamallahu ujurana bi musabina bi Amirulmuminin (AS)”.

Kuma a gabanmu, jibi Juma’a akwai Ranar Quds na duniya, wanda akan nuna goyon baya ga al’ummar Palasdinu kan ta’asar da ake musu a mamayar da aka musu. To kuma na bana, ya zama ya fita daban da na sauran shekaru. Saboda tun kamawar Rajab, mutanen nan (isra’iliyawa) sai sun yi kisan kai. Kullum sai an kashe Bapalasdine. Wannan al’amari yana da ban-al’ajabi. Kuma da Ramadan ya kama sai aka shiga tsanantawa, yanzu Masjidul Aqsa ne za su je su tarwatsa masu sallah, basu damu ba su kakkama mutane su daddaure. Hotuna na iya nunawa idan mutane sun damu da su gani.

To, a bara mun karfafa guiwar mutane a kan nuna ‘Tadamuni’ da al’ummar Palasdinu. Akwai wani abu da ake yayin cewa a rika daga tutar Palasdinu, suna cewa; #FlyThePalasdinianFlag. To kuma Alhamudulillahi, ‘yan uwa a muzaharorinsu a nan Abuja duk su kan rika daga tutar Palasdinu ko da ma muzaharar suna yi a kan wani abu ne, ranakun Litini da ranar Juma’a da wasu raneku da su kan yi Muzaharori, duk suna rika daga tutoci. Saboda haka yana da kyau a daidai wannan lokaci a rika daga wadannan tutoci na nuna cewa muna tare da al’ummar Palasdinu.

Nuna muna tare da al’ummar Palasdinu nuna muna tare da wani abu ne da ya dame mu duk cikarmu, domin Palasdinawan nan da ake ta faman kashewa, a madadinmu suke wannan gwagwarmaya, – a madadin dukkan al’ummar Musulmi ne. Domin kuwa wadanda suke musu abin da suke musu, idan suna iyawa, to za su yi ma kowa da kowa. Kuma basu ma boye ba, akwai wani makiyin Allah makiyin Annabi (S), wanda yake cewa wai yakin duniya na uku, duk wanda ma bai ce yana nan tafe ba, kamar bai san abin da yake yi bane. Wai yana nan tafe. Kuma a lokacin yace, za su kona Musulmi. Za su kona Larabawa. Bai ko boye ba. Yace, za su kona su ne kurmus. Haka yace.

Kila za ku san shi, baro-baro yake wannan maganar. Saboda haka su abin da suke tunani shine, su za su yi fada ne da al’ummar Musulmi gaba daya. Kuma hankoronsu ba Palasdinu ne kawai ba, za su kafa daular isra’ila ce da za ta mamaye dukkanin wannan yankunan, wanda ya hada kasashen Palasdinu, da Urdu, da Syria da Arewacin kasar da ake ce ma Saudi Arabiyya, har da Birnin Madina.

Su a wajensu wai suna cewa wai Birnin Madina ma wai birninsu ne, wai da Yahudawa ne a wajen kafin wai Annabi (S) ya je ya kore su. Ko da yake ba Annabi suke ce masa ba. Wai ya je ya kore su. Kamar yadda suke cewa wai ya karkashe su ya kore su a kasar, wai kasarsu ce. Saboda haka sun zana taswira wanda suka saka Madina a ciki, su a wajensu za su mamaye wannan wajen ne, kuma tunaninsu kenan. Insha Allahu wannan mafarki nasu ba zai taba yiwuwa ba. Amma kuma dai mafarki ne kuma suna ta ta’asarsu.

Saboda haka, ya kamata duk al’ummar Musulmi su nuna damuwarsu. A yi shirin wannan Ranar Quds, a yi ta a ko ina. Mun san cewa da mun zabi wadansu birane ne musamman muka ce a nan ne za a yi Quds, da kamar birni 22 muke yi, to amma saboda irin yanayin tsaro da aka jefa kasar nan a ciki, wanda tafiye-tafiye ma da wahala, saboda haka sai ya zama wadansu birane ma da ba a saba yi ba duk an yi bara, bana ma haka nan. Saboda haka za a iya yi a biranen da ma ba a saba yi ba. In zai yiwu, yana da kyau a je a yi a manyan birane, in ma ba zai yiwu ba, wadansu biranen da ba a saba yi ba ma du kana iya yi. Ba kamar Ashura da muka ce ko a kauyuka za a iya yi ba, ita ranar Quds ranar ‘Tadamun’ ne, kamata ya yi ita duniyar ta gani muna tare da su, (don haka) za a yi a muhimman wurare.

Ba kuma kawai ranar Quds ne za mu nuna ‘Tadamuni’ da al’ummar Palasdinu ba, duk wannan lokacin da ake musu wannan ta’asar ya kamata mu nuna, tunda sauran duniya ma suna yi. Idan mutum yana bibiyan labaru zai ga a sauran biranen duniya, duk an ta fitowa ana nuna rashin goyon baya ga irin ta’asar da ake ma al’ummar Palasdinu a wannan wata mai tsarki na Ramadan. Saboda haka bai Kaman a ce mu sai ranar Quds din ne kawai za mu yi ba, a kowane lokaci ma ya kamata ya zama muna nuna ‘tadamun’, a zantukanmu da kalamanmu da rubuce-rubucenmu a jaridu, da kuma shafuffuka na yanzu (da ake) zamanin ‘internet’, da kuma wakoki da ire-irensu, duk a rika tunatar da al’umma, a fadakar da ita kan abin da ke faruwa a al’ummar Palasdinu, ya zama ya shafe mu gaba dayanmu.

Ina fatan mu ga sauyi insha Allahu. Kuma sauran al’umma da suke kallon abin na wasu ne, to muna fatan Allah Ya fadakar da su, su gane cewa na kowa da kowa ne.

Wasallallahu ala Muhammadin wa ala alihid Dahirin.
Wassalamu alaikum wa rahmatullahi Ta’ala wa barakatuhu.

Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky ya gabatar da wannan jawabin ne ranar Laraba 21 ga Ramadan, 1444 (12/4/2023) a gidansa da ke Abuja, inda aka yada ta kafafen sadarwa. Cibiyar Wallafa ta rubuto daga sautin.

 

Ga sautin jawabin nan:

Jawabin Jagora kan Quds din 1444 – 2023

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai

Yadda Jagora Shaikh Zakzaky Ya Yi Musharaka Da ‘Yan Uwa A Yayin Tattakin Arbaeen Zuwa Karbala

Published

on

Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya yi musharaka a cikin Tattakin Yaumul Arbaeen da ake yi a ƙasar Iraki, a yau Alhamis 17 ga Safar 1446 (22/8/2024).

Tare da yadda ya rika rabawa al’ummar da ke Tattakin daga Najaf zuwa Karbala hadiyyar abinci da hannunsa masu albarka, don hidimtawa maziyartan Imam Husaini (AS), a Maukibin Ofishinsa da ke Amudi na 1117 a kan hanyar.

Wannan shi ne karo na farko da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya halarci taron Arbaeen din Imam Husaini (AS) a haraminsa da ke Karbala, wanda za a gudanar da taron a ranar Lahadi mai zuwa. Duk da a baya Jagoran ya sha ziyartan makwancin Imam din a lokutan baya, amma ba a daidai lokacin Arbaeen ba.

Za ku iya ganin kuma wasu Hotunan Jagoran, a yayin da ya halarci Maukibin Tariƙatul Husain, a ranar Laraba 16 ga Safar da daddare, inda ya gabatar da jawabi akan yadda sadaukarwar Imam Husaini (AS) ta kawo juyi ga duniyar Musulmi zuwa ga sahihin addini.

Continue Reading

Labarai

Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky Ya Isa Birnin Karbala

Published

on

A ranar Lahadi 12 ga watan Safar 1446 ne Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya bar gida Nijeriya zuwa birnin Karbala Mai Tsarki, don yin Musharaka a taron Yaumul Arbaeen na Imam Husaini (AS) na wannan shekarar, tare da tawagarsa.

Ranar Talata, 14 ga Safar, jami’an Ataba Husainiyya suka tarbe shi a Haramin Imam Husaini (AS) da ke birnin na Karbala. A yayin ziyarar ya gana da Sheikh Abdul Mahdi Karbalai, inda suka tattauna batutuwan da suka shafi yada koyarwar Ahlulbaiti a cikin al’umma.

Wannan ne karo na biyar da Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya je ƙasar ta Iraqi domin ziyarar Limaman Shiriya da Mashhadodinsu ke kasar, sai dai kuma shi ne karo na farko da Jagoran ya je a daidai lokacin da ake gudanar da taron Yaumul Arbaeen, inda miliyoyin maziyarta ke zuwa daga sassa daban-daban na fadin duniya.

Daga tawagar da ke gudanar da Tattaki, musamman daga birnin Najaf zuwa Karbala a duk shekara, akwai tawagar mutanen Nahiyar Afirka, musamman ‘yan Nijeriya, almajiran Shaikh Zakzaky da suke karatu a can, da kuma daruruwan da suke tafiya duk shekara daga nan kasar zuwa kasar Iraq din musamman don wannan, kuma a ranar Lahadin su ma suka fara yin Tattakin daga birnin Najaf, inda suka nufi Karbala, ana sa ran isarsu kafin ko zuwa ranar Arbaeen, wanda za ta fado ranar Lahadi mai zuwa.

Akwai Maukibi da aka tanada musamman don yin hidima ga maziyartan Imam Husaini (AS), wanda ke gudana karkashin ofishin Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a Amudi na 1117, inda dimbin al’umma ke ziyarta suna karban Hadiyya, tare da yi na Jagora addu’a ta musamman.

A gida Nijeriya ma, gobe Laraba ‘yan uwa almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky za su fara gudanar da Tattakin, don misaltawa daga sassa daban-daban na fadin kasar, inda ake sa ran za a rufe a ranar Lahadi, wadda ta dace da ranar Arbaeen din Imam Husaini (AS) na bana, a birnin tarayya, Abuja.

Ga wasu daga hotunan tarbar Jagora, wanda shafin ofishinsa suka wallafa a yau Talata.

 

Continue Reading

Labarai

An Yi Taron Bikin Idil Ghadir A Abuja

Published

on

Harkar Musulunci a Nijeriya, ƙarkashin Jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), ta gudanar da gaggarumin bikin tunawa da ranar da aka naɗa Imam Ali (AS) a matsayin Khalifa kuma Magajin Annabi (S) a bayansa.

Taron wanda ya gudana a garin Abuja, a ranar Talata 18 ga watan Zulhijja 1445, daidai da 25 ga watan June 2024. Sheikh Zakzaky ne ya zama Babban Baƙo mai jawabi a wajen taron.

Ga Hotunan taron:

Continue Reading

Trending

Copyright © 2019 By Institute for Compilation and Publication of Sheikh Zakzaky's Works.