Labarai
Tattakin Arba’een 1445 Daga Yankunan Maraba Da Suleja Zuwa Abuja
Ranar Talata 19 ga watan Safar 1445 (5/8/2023) ne Harkar Musulunci a karkashin Jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ta gudanar da Tattakin Yaumul Arba’een din Imam Husaini (AS) a yankuna biyu da suke zuwa birnin Abuja.
Yankunan guda biyu su ne; Yankin Maraba, wanda ya tattaro ‘yan uwan da suka saba yin Tattaki a Zangunan Pambegua da Kano zuwa Zariya, da kuma ‘yan uwan da suka fito daga yankin Abuja, wanda ta hado Kogi, Lokoja, Ilorin, Lagos, Ibadan, Abuja da yankunansu. Sai Yanki na biyu, su ne suka taso daga garin Suleja, wanda suka hada ‘yan uwan da suka saba yin Tattaki daga Zangunan Malumfashi, Funtua, Kaduna da Birnin Gwari zuwa Zariya.
An gudanar da Tattakin Abuja ne bayan da kowane yanki suka gudanar da Tattakin da suka saba gudanarwa a Zangonninsu zuwa Zariya daga ranar Asabar zuwa Litini, ranar Talata sai aka hadu a Abuja don Tattakin na bai-daya.
An kammala Tattakin na yankunan Maraba da Suleja lafiya, duk kuwa da barazanar da sojoji gami da ‘yan sanda suka rika yi a lokacin da Tattakin ke gudana a yankin Maraba.
Ga wasu daga hotunan Tattakin Yankin Maraba-Abuja:
Ga wasu daga hotunan Tattakin Yankin Suleja-Abuja:
Labarai
Yadda Jagora Shaikh Zakzaky Ya Yi Musharaka Da ‘Yan Uwa A Yayin Tattakin Arbaeen Zuwa Karbala
Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya yi musharaka a cikin Tattakin Yaumul Arbaeen da ake yi a ƙasar Iraki, a yau Alhamis 17 ga Safar 1446 (22/8/2024).
Tare da yadda ya rika rabawa al’ummar da ke Tattakin daga Najaf zuwa Karbala hadiyyar abinci da hannunsa masu albarka, don hidimtawa maziyartan Imam Husaini (AS), a Maukibin Ofishinsa da ke Amudi na 1117 a kan hanyar.
Wannan shi ne karo na farko da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya halarci taron Arbaeen din Imam Husaini (AS) a haraminsa da ke Karbala, wanda za a gudanar da taron a ranar Lahadi mai zuwa. Duk da a baya Jagoran ya sha ziyartan makwancin Imam din a lokutan baya, amma ba a daidai lokacin Arbaeen ba.
Za ku iya ganin kuma wasu Hotunan Jagoran, a yayin da ya halarci Maukibin Tariƙatul Husain, a ranar Laraba 16 ga Safar da daddare, inda ya gabatar da jawabi akan yadda sadaukarwar Imam Husaini (AS) ta kawo juyi ga duniyar Musulmi zuwa ga sahihin addini.
Labarai
Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky Ya Isa Birnin Karbala
A ranar Lahadi 12 ga watan Safar 1446 ne Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya bar gida Nijeriya zuwa birnin Karbala Mai Tsarki, don yin Musharaka a taron Yaumul Arbaeen na Imam Husaini (AS) na wannan shekarar, tare da tawagarsa.
Ranar Talata, 14 ga Safar, jami’an Ataba Husainiyya suka tarbe shi a Haramin Imam Husaini (AS) da ke birnin na Karbala. A yayin ziyarar ya gana da Sheikh Abdul Mahdi Karbalai, inda suka tattauna batutuwan da suka shafi yada koyarwar Ahlulbaiti a cikin al’umma.
Wannan ne karo na biyar da Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya je ƙasar ta Iraqi domin ziyarar Limaman Shiriya da Mashhadodinsu ke kasar, sai dai kuma shi ne karo na farko da Jagoran ya je a daidai lokacin da ake gudanar da taron Yaumul Arbaeen, inda miliyoyin maziyarta ke zuwa daga sassa daban-daban na fadin duniya.
Daga tawagar da ke gudanar da Tattaki, musamman daga birnin Najaf zuwa Karbala a duk shekara, akwai tawagar mutanen Nahiyar Afirka, musamman ‘yan Nijeriya, almajiran Shaikh Zakzaky da suke karatu a can, da kuma daruruwan da suke tafiya duk shekara daga nan kasar zuwa kasar Iraq din musamman don wannan, kuma a ranar Lahadin su ma suka fara yin Tattakin daga birnin Najaf, inda suka nufi Karbala, ana sa ran isarsu kafin ko zuwa ranar Arbaeen, wanda za ta fado ranar Lahadi mai zuwa.
Akwai Maukibi da aka tanada musamman don yin hidima ga maziyartan Imam Husaini (AS), wanda ke gudana karkashin ofishin Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a Amudi na 1117, inda dimbin al’umma ke ziyarta suna karban Hadiyya, tare da yi na Jagora addu’a ta musamman.
A gida Nijeriya ma, gobe Laraba ‘yan uwa almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky za su fara gudanar da Tattakin, don misaltawa daga sassa daban-daban na fadin kasar, inda ake sa ran za a rufe a ranar Lahadi, wadda ta dace da ranar Arbaeen din Imam Husaini (AS) na bana, a birnin tarayya, Abuja.
Ga wasu daga hotunan tarbar Jagora, wanda shafin ofishinsa suka wallafa a yau Talata.
Labarai
An Yi Taron Bikin Idil Ghadir A Abuja
Harkar Musulunci a Nijeriya, ƙarkashin Jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), ta gudanar da gaggarumin bikin tunawa da ranar da aka naɗa Imam Ali (AS) a matsayin Khalifa kuma Magajin Annabi (S) a bayansa.
Taron wanda ya gudana a garin Abuja, a ranar Talata 18 ga watan Zulhijja 1445, daidai da 25 ga watan June 2024. Sheikh Zakzaky ne ya zama Babban Baƙo mai jawabi a wajen taron.
Ga Hotunan taron:
-
Makaloli12 months ago
Labarin Fitina Tawayiyya A Takaice
-
Labarai3 months ago
Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky Ya Isa Birnin Karbala
-
Labarai5 months ago
An Yi Taron Bikin Idil Ghadir A Abuja
-
Labarai5 months ago
Jagora Sayyid Zakzaky (H) Ya Yanka Ragonsa Na Layya
-
Bidiyo6 months ago
Shaikh Zakzaky Ya Yi Ta’aziyyar Shahadar Shugaban Iran, Ebraheem Ra’isi
-
Labarai6 months ago
Jagora Sheikh Zakzaky (H) Ya Gana Da Dandalin Ɗalibai A Ranar Tunawa Da Imam Khomeini
-
Labarai6 months ago
A Yayin Bikin Tunawa Da Auren Imam Ali (As) Da Sayyida Zahra (As), Jagora Sheikh Zakzaky (H) Ya Gana Da Dandalin Matasan Sharifai
-
Labarai3 months ago
Yadda Jagora Shaikh Zakzaky Ya Yi Musharaka Da ‘Yan Uwa A Yayin Tattakin Arbaeen Zuwa Karbala